Coronavirus: NEMA ta bukaci a hana siye da siyar da kayan gwanjo

- Hukumar kula da al'amuran karta-kwana ta kasa (NEMA) tayi kira ga jama'ar Najeriya da su kiyayi shigowa da kuma siyen kayan gwanjo

- Kamar yadda shugaban hukumar na jihohin Imo da Abia ya sanar, ya ce ci gaba da shigo da kayan tamkar gayyatar mugunyar cutar coronavirus ne cikin kasar nan

- Ya yi kira ga gwamnatin tarayya a kan ta gaggauta hana shigo da kayan gwanjon tare da hukunta duk wanda ta kama da laifin hakan

Hukumar kula da al'amuran karta-kwana ta kasa (NEMA) tayi kira ga 'yan Najeriya a kan su daina shigowa da kuma siyan kayan gwanjo don gujewa mugunyar cutar Coronavirus a kasar nan.

Hukumar tayi wannan kiran ne a ranar Lahadi a wani horarwa da shugaban cibiyar na yankin jihohin Imo da Abia, Evans Ugoh, ya shirya.

A yayin jawabi a taron horarwar, Ugoh ya bayyana cewa Najeriya na ci gaba da gayyato cutar cikin kasar nan ne matukar aka ci gaba da shigowa tare da siyan kayan gwanjon, kamar yadda jaridar Information.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Jennifer Haller: Mace ta farko a duniya da aka fara gwada maganin Coronavirus a jikinta

Ugoh ya ci gaba da kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya a kan ta hana shigowa da kayan gwanjon cikin kasar nan ta hanyar hukunta duk wadanda aka kama da laifin hakan.

A wani labari na daban, wata mata mai shekaru 43 a duniya ta zama mutum ta farko a duniya da aka yiwa allurar gwajin maganin cutar Coronavirus Bayan fara gabatar da gwajin, Jennifer Haller ta zama ta farko da aka fara gabatar da gwajin a jikinta.

Gwajin wanda aka fara shi kwanan nan, Dr Lisa Jackson ta jagoranci gwajin, wacce take babbar ma'aikaciya a cibiyar lafiya ta Seattle dake birnin Washington, birnin da yafi ko ina yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar Amurka, inda mutane 42 suka mutu a cikin mutane 69 na kasar.

Jennifer Haller ta yi magana akan wannan gwaji da aka gabatar a kanta, inda ta ce: "Hankalin mu duka a tashe yake saboda wannan cutar, saboda haka nake ganin kamar wannan wata dame ce a wajena a fara gabatar da gwajin a kaina."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHB9kmppcWphYrCwvs6nmK%2BhoqrAbrrEpphmrJFir7a3wJygZpldna6vrYysoLKdXZmubr%2FIspirZZSWeqyt2JqlZp%2Bnlruru42hq6ak